Harbe-harbe a kasar Faransa | Labarai | DW | 25.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harbe-harbe a kasar Faransa

Rahotanni daga kasar Faransa na nuni da cewa mutane uku sun rasa rayukansu yayin da wasu hudu kuma suka jikkata sakamakon harbi da wani mutum ya yi da bindiga.

Jami'an 'yan sandan Faransa a Roye

Jami'an 'yan sandan Faransa a Roye

Wani mutum ne dai ya bude wuta a sansanin 'yan gudun hijira na gypsy da ke arewacin kasar tare da hallaka mutanen uku. Mahukuntan kasar ta Faransa sun sanar da cewa mutanen da suka rasa rayukansu sun hadar da wani mutum da mace guda da kuma wani dan karamin yaro, yayin da dan bindigar ke zaman daya daga cikin mutane hudun da suka jikkata. Kawo yanzu dai ba a tabbatar da abin da ya janyo wannan hargitsi da ya afku a garin Roye da ke kimanin kilomita 110 da arewacin Pari babban birnin kasar ba. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da babban mai gabatar da kara na kasar Francois Molins ya bayyana cewa za su tuhumi dan kasar Morokon nan da ya yi harbi a jirgin kasa na kasar a karshen mako Ayoub El-Khazzani mai kimanin shekaru 26 a duniya da laifin ta'addanci.