Haramta sayan man fetur da ′yan tawayen Libiya suka yi safara zuwa ketare | Labarai | DW | 20.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haramta sayan man fetur da 'yan tawayen Libiya suka yi safara zuwa ketare

Majalisar Dinkin Duniya ta haramtawa kasashen duniya sayan man fetur da ya fito daga hannun 'yan tawayen Libiya.

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da sabon kudirin da ya baiwa kasashen duniya izinin cafke duk wani jirgin ruwan dakon man fetur da suke zargin yana dauke da gurbataccen man fetur da aka fitar dashi daga Libiya ta haramtacciyar hanya. Wannan kudirin da kwamitin sulhun ya amince dashi a wannan Larabar (19. 03. 2014), ya bayar da dama ga kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su cafke jirgin, kana su mayar da man fetur din ga gwamnatin kasar ta Libiya. Matakin dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da Amirka ta dakatar da wani jirgin ruwan dakon man fetur - mallakar kasar Cyprus, wanda 'yan tawayen kasar ta Libiya ke ta yin amfani dashi wajen safarar man fetur zuwa ketare ta haramtacciyar hanya. An dauki tsawon lokaci ana sa-in-sa a tsakanin gwamnatin Libiya da kuma 'yan tawayen kasar, bayan da suka karbe ikon gudanar da wasu tashoshin jragen ruwan da ake hako man fetur - har guda uku a shekarar da ta gabata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab mohammed Abubakar