Har yanzu ba´a tabbatar da yawan mutanen da suka rasu a fashewar bututun mai a Nijeriya ba | Labarai | DW | 27.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu ba´a tabbatar da yawan mutanen da suka rasu a fashewar bututun mai a Nijeriya ba

Kwana guda bayan fashewar wani bututun mai a Legas cibiyar hada-hadar kasuwanci a tarayyar Nijeriya, har yanzu ba´a tantance yawan mutanen da wannan mummunan bala´i ya rutsa da su ba. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce mutane 269 suka rasu amma yawan su ka iya karuwa. Su kuwa kamfanoni dillancin labaru sun ce yawan wadanda suka mutu ya kai mutum 850. Majiyoyin hukuma sun ce barayin mai ne suka fasa bututun don kwasar mai a unguwar Agbule Egba dake wajen birnin na Legas. Sannan daga bisani daruruwan mutane sun shiga layi don kwasar ta su ganima, lokacin da bututun ya yi bindiga.