1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Najeriya: Ana dakon sakamakon zabe

Abdoulaye Mamane Amadou
February 24, 2019

Akwai wasu jihohin Najeriya da ake gudanar da zabe a wannan Lahadi a sanadiyar matsaloli da aka samu a jiya, a yayin da wadanda suka kamalla zaben ke zaman jiran sakamakon zaben daga hukumar zabe ta kasa.

https://p.dw.com/p/3E0AU
Wahl in Nigeria
Hoto: picture alliance/AP/Sunday Alamba

Mutum kusan miliyan 72 aka kiyasta sun yi zabe. Rahotanni daga kasar sun ce yanzu haka Hukumar INEC na cigaba da tattara sakamakon tashoshin zabe dubu 120 000, daga jihohin kasar 36, duk da ya ke da akwai wasu runfunan zaben, da hukumar ta ce jama'a za su sake komawa a yau Lahadi domin jefa kuri'a, biyu bayan samun wasu matsaloli.

Duk da ya ke 'yan takara akalla 70 suka shiga takara, amma fafatawar ta fi zafi ne a tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da abokin hamayyarsa na PDP Abubakar Atiku.

Kafin dan takara ya lashe zaben na shugaban kasa, ana son dole  ya samu kashi 25 cikin dari na adadin kuri'un da aka jefa ko biyu bisa uku na jihohi 36 na kasar. Akalla kujerun 'yan majalisun kasar 469 ake shirin sauyawa ciki har da na 'yan majalisun dattijai na Tarayyar ta Najeriya.