Hanyar neman dakile rikicin Libiya | Labarai | DW | 26.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hanyar neman dakile rikicin Libiya

Hukumomin Italiya sun tattauna da wakillan yankuna na kasar Libiya kan matsalar safarar bakin haure domin samun matakan magance yanayin da ake ciki.

Ministan tsaron cikin gidan kasar Italiya Marco Minniti, ya tattauna a birnin Roma da wakillai da dama na kudancin kasar Libiya kan batun matakan taimakon yankin domin shayo kan matsalar masu fataucin bakin haure da ke zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya.

Cikin wata sanarwa da ya karanta, ministan cikin gidan na Italiya ya ce masu safarar bakin haure dai sun kasance manyan makiya na Italiya da kuma Libiya, kuma bai katama a ce sun samu wuri a cikin kasar Libiya da ke kokarin samun cikeken tsari na bin dokoki da kare incin dan Adam ba.

Wannan zaman taro dai ya wakana ne bayan wata tattaunawar farko da suka yi a watan Febrairu, da kuma wani taro irin wannan da ya gudana tare da ministan cikin gidan na Italiya a birnin Tripoli, inda ake kokarin ganin masu fada a ji a yankunan kasar ta Libiya sun taimaka an samu toshe hanyoyin da masu safarar bakin hauren ke bi, inda ita kuma kasar ta Italiya ta dauki alkawarin biyan wasu ayyukan bunkasa rayuwar al'ummomin yankin tare da ban hannun Tarayyar Turai.