1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hankula sun kwanta a Thailand

July 18, 2018

Yaran nan 'yan kwallon kafa na kasar Thailand da aka ceto daga wani kogo, sun yi bayyanarsu ta farko.

https://p.dw.com/p/31fLK
Thailand PK des geretteten Fußtball-Teams
Hoto: Reuters/S. Zeya Tun

A wannan Larabar ce yaran nan 'yan kwallon kafa na kasar Thailand tare da kocinsu da aka ceto a kwanakin baya, daga wani kogo, sun yi bayyanarsu ta farko.

Sanye da rigunan wasanni masu launin fari da kore, an nuno su cikin annashuwa a wannan Larabar, a birnin Chiang Rai na kasar ta Thailand.

Yaran su 12 da kocin na su, sun fito bainar jama'a ne lokacin wani taron manema labarai, mako guda bayan nasarar kubutar da su da wasu gwanayen nutso suka yi.

Tun bayan ceto su da aka yin dai sun kasance karkashin kulawar likitoci da masana halayyar dan Adam, wadanda suka tabbatar da sun dawo hayyacinsu, saboda tsananin tashin hankali da suka yi fama da shi.