1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hamas ta amince da tayin tsagaita wuta a Gaza

May 6, 2024

Kungiyar Hamas mai iko da zirin Gaza na Falasdinu ta sanar da amincewa da tayin tsagaita wuta da kasashen Qatar da Masar da ke shiga tsakani a rikicin suka mika mata.

https://p.dw.com/p/4fYsQ
Shugaban Hamas Ismail Haniyeh
Shugaban Hamas Ismail Haniyeh Hoto: Iranian Presidency Office/ZUMAPRESS.com/picture alliance

Masu aiko da rahotanni daga yankin sun ce jim kadan bayan sanar da wannan mataki da aka dade ana jira jama'a sun fantsama kan titunan birnin Rafah inda suka yi ta raye-raye na nuna murna har ma da harba bindiga a sarararin samaniya.

Karin bayani: Biden: Fata kan tsagaita wuta a Gaza

Wani jigo a kungiyar ta Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa yanzu zabi ya rage ga Isra'ila bayan da kungiyar ta bayyana cewa ta amince da tayin sulhun da kasashen Qatar da Masar da ke kai komo wajen shiga tsakani a rikicin Gaza suka gabatar mata.

Karin bayani: Isra'ila da Hamas za su sake hawa kan teburin sulhu

Sai dai jim kadan bayan fidda wannan sanarwa, an ambato wani jigo a gwamnatin Isra'ila na cewa ba za su lamince da wasu tanade-tanade da daftarin yarjejeniyar ta kunsa ba.