Hamas ta amince da sakin fursunonin yaki
October 4, 2025
Mayakan na Hamas sun kuma amince da mika dukkan fursunonin yakin Isra'ila da ke raye tare kuma da dukkan gawarwakin wadanda suka mutu a hannunsu ga hukumomin Tel Aviv. Kazalika kungiyar ta ce za ta shiga cikin tattaunawar wanzar da zaman lafiyar yankin tare kuma da yin nazari kan daftarin da Trump ya gabatar.
Mazauna Gaza sun wayi gari cikin farin ciki
Al'ummar Gaza a karon farko sun wayi gari cikin farin ciki ba tare da jin rugugi daga sararin samaniyar yankin ba, inda haske ya mamaye sararin samaniyar Gaza a wannan Asabar ba tare da duhun hayakin bama-bamai da makamai masu linzami ba, biyo bayan daftarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na kawo karshen luguden wutan da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza.
Ko shawarar Trump za ta kawo karshen yaki a Gaza?
Jamila al-Sayyid daya daga cikin al'ummar Gaza ta ce tayi matukar mamakin matakin da Trump ya dauka na tsagaita bude wuta, kasancewar a kullum yana tare da Isra'ila, haka shi ma wani mazaunin yankin Mahmud Abu Shamala, ya ce tsagaita wutar ya zo masa tamkar a mafarki to amma hannun agogo na iya komawa baya idan har Hamas bata saki dukkan fursunonin yakin Isra'ila ba.
Kudurori a sabon daftarin Donald Trump
Kudurorin Trump guda 20 kan yankin na Gaza sun hadar da dakatar da tsagaita bude wuta nan take da musayar fursunonin yakin bangarorin biyu da kuma janyewar dakarun Isra"ila daga Gaza sauran kudurorin sun hada da kwance damarar makaman Hamas da kuma nada kantoman da zai jagoranci sake gina yankin, sannan kuma shugaban Donald Trump ya yi kira ga kungiyar Hamas da ta gaggauta amincewa da bukatar zaman lafiyar yankin ko kuma ya murkushe kungiyar.
Isra’ila na shirin fuskantar zanga-zanga a kan yakin Gaza
Hamas da kasashen duniya ciki har da Amurka da Jamus da Tarayyar Turai ke yi wa kallon yar ta'adda na rike da 'yan Isra'ila akalla 48 da ake hasashen 20 daga cikinsu na raye. Tuni dai kungiyar Hamas ta amince da bukatar zama a teburin sulhu tare da amincewa da sakin dukkan fursunonin yakin Isra'ila.