1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas da Fatah sun kalubalanci shirin Isra'ila

Gazali Abdou Tasawa
July 2, 2020

Kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa na Hamas da Fatah sun sanar da shirin hada kai domin kalubalantar shirin Isra'ila na mallake fadamar Jodan da ke a yankin yammacin kogin Jodan wanda dama Isra'ilar ta mamaye.

https://p.dw.com/p/3egyt
Gazastadt I Palästinensische Anhänger der Fatah-Bewegung
Hoto: picture-alliance/M. Ajjour

Kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa na Hamas da Fatah sun sanar da shirin hada kai domin kalubalantar shirin Isra'ila na mallake fadamar Jodan da ke a yankin yammacin kogin Jodan wanda dama Isra'ilar ta mamaye.

 Kungiyoyin Palasdinawan wadanda ga al'ada ke hamayya da juna sun bayyana wannan aniya tasu ce a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da babban magatakardan kungiyar ta Fatah Jibril Rajoub da Saleh Al-Arouri wani kusa na kungiyar ta Hamas suka shirya ta kafar bidiyo daga birnin Beyrouth.

 Gwamnatin Isra'ila ta sanar da soma aiwatar daga ranar daya ga watan Yulin nan da shirin wanda Amirka ce ta fito da shi da sunan sasanta rikicin Palasdinawa da Isra'ila, wanda ya tanadi bai wa Isra'ilar 'yancin mallakar garuruwan share zauna da fadamar yammacin kogin Jodan da Isra'ilar ta mamaye tun a shekara ta 1976, da kuma kafa kasar Paladinu a tsanain yammacin kogin Jodan da zirin Gaza.