Hama Amadou ya tsere zuwa Faransa | Labarai | DW | 01.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hama Amadou ya tsere zuwa Faransa

Shugaban majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar da ake zargi da hannu a badakalar fataucin kananan yara, ya tsere zuwa kasar Faransa.

Shugaban majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar Hama Amadou wanda ya fice daga kasar bayan tube masa rigar domin amsa tambaya bisa safarar jarirai yanzu haka yana kasar Faransa.

Wata majiya ta kusa da Shugaban Burkina Faso ta tabbatar da cewa Hama Amadou ya fice daga kasar inda ya fara zuwa tun farko zuwa Faransa, domin samun mafaka. Majiyar ta ce yanzu haka shugaban majalisar dokokin ta Nijar din yana birnin Paris, yayin da matarsa da wasu mutane 17 da suka hada da ministan aikin gona Abdou Labo ke tsere a gidan kurkuku, bisa zargin safarar jirirai daga makwabciyar kasar ta Najeriya.

Magoya bayan Amadou suna zargin Shugaban Jamhuriyar ta Nijar Mahamadou Issoufou da yi masa yarfen siyasa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal