Halin da ake ciki a yankin Darfur | Labarai | DW | 16.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a yankin Darfur

Hukumar Majalisar Dinkin Dunia, mai kula da bada taimakon abinci wato PAM, ta ambata rage tallafin da ta ke baiwa yankin Darfur na ƙasar Sudan, a dalili da ƙarancin kuɗaɗe.

Bayan wannan sanarwa, gwamnatin ƙasar Sudan, ta ambata cike giɓin da za a samu na abinci.

Mataimaki shugaban ƙasa Ali Osman Taha, ya sanar manema labarai cewa, gwanatin Sudan, za ta kai agajin tonne dubu 20, na cimaka a wannan yanki da ke fama da rikicin tawaye.

Gwamnatin Sudan, zata bada wannan agaji, a tsawan watani 3 masu zuwa.

A halinda ake ciki kuma Komiti sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya bi sahun kungfiyar tarayar Afrika,a game da matsa ƙaimi, ga yan tawaye da gwamnatin Sudan ,domin su tabbatar da aikata yarjejeniyar da su ka rattaba hannu a kai, a birnin Abjua.

Sannan ɓanagarori 2, na yan tawaye da su ka ƙauracewa yarjejeniyar su cenza tunani.