HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 06.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

HOTON MUTUMIN DA AKE CEWA AN CAFKE WATO IBRAHIM IZZAT AL DAOURI;TSOHON MINISTAN TSARO NA IRAQI.

default

Batun rashin harkokin tsaro a iraqi har yanzu na nan jiya a yau,a maimakon a samu raguwar sa sai ma kara hauhawa yake tamkar farashi.

A misali dazu dazun nan muka samu rahoton tashin wani bom a wajen garin falluja wanda sakamakon hakan yayi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar Amureka da daman gaske,banda kumqa wasu da yawa da suka jikkata.

Gamsassun bayanai da suka iso mana sun tabbatar da cewa tashin wan nan bom nada alaka da wani hari da yan fadan sari ka noke suka kai kann rundunar sojin na Amurka dake da sansani a wajen garin na falluja.

Bugu da kari rahotanni sun nunar da cewa a sabili da rashin sanin taka mai mai yadda za a shawo kann al,amarin tsaro a garin ya haifar sojin na Amurka sun mayar da harkokin tabbatar da tsaron hannun tsoffin jamian tsaro na gwamnatin Saddam Hussain dake yankin,to amma kuma duk da hakan kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Ya zuwa yanzu dai bayanai da suka iso mana sun tabbatar da cewa sojojin kasar Amurka dake jibge a kasar ta iraqi sun rasa gano bakin zaren yadda zasu tafiyar da harkokin tabbbatar da zaman lafiya a wan nan yanki na falluja.

Hakan kuwa a cewar masu nazarin abin da kaje yazo na yankin nada nasaba da rashin hadin kai da basu samu ba ne daga gurin mabiya darikar shiawa dake da sansani a wamn nan gari.

A yayin da ake cikin wan nan yanayi a garin na falluja a daya wajen kuma baya nai daga kasar ta iraqi sun shaidar da cewa yan fadan sari ka noke na kasar sun sako mutumin kasar turkiyyar nan da sukayi garkuwa dashi.

Shi dai wan nan mutumi a cewar bayanai ya kasance matukin babbar mota ne dake gudanar da aikin wata kwangila a kasar ta iraqi.

Tsallake rijiya da bayan da baturken yayi ya biyo bayan alkawari ne da kamfanin da yakewa aiki sukayi ne cewa zasu janye yin aiki a kasar kamar yadda yan fadan sari ka noken suka bukaci da suyi.

Ya zuwa yanzu dai akwai yan kasar ta turkiyya guda biyu matukan babbar mota da suka rugamu gidan gaskiya sakamakon aiyuka na yaqn fadan sari ka noke a tsawon kusan watanni biyu da suka gabata.

A wata sabuwa kuma har yanzu akwai shakku game da bayanin cewa an kame Izzat Ibrahim Al Daouri tsohon na hannun daman Saddan hussain a can garin Tikrit.

A cewar ministan tsaron kiasar ta iraqi Hazim Al shalaan babu kanshin gaskiya game da cewa Ibrahim Al daouri na hannun jamian tsaron kasar ta iraqi.

Wan nan dai bayani na ministan tsaron kasar ya saba da bayanin da kakakin sa ya bayar a baya na cewa jamian tsaron kasar sun cafke na hannun daman tsohon shugaba Saddam Hussain.

A yanzu haka dai bayanai sun shaidar da cewa za a gudanar da bincike na aune aune kann mutumin da ake tsare dashi don tabbatar da cewa ko Izzat Ibrahim din ne ko kuma aa,wanda jiran yin hakan ne ya hana rundunar mamaye da Amurka kewa jagoranci tabbatar da labarin cafke tsohon shugaban,wanda a can baya ya kasance na hannun daman Saddam Husasain.

Ibrahim Sani.