Halin da a ke ciki a Irak | Labarai | DW | 10.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da a ke ciki a Irak

A ƙalla mutane 3 su ka rasa rayuka da dama su ka jikkata, a hare haren ƙunar baƙin waken da su ka rista yau, da birnin Bagadaza na ƙasar Iraki.

Wannan sabin hare haren, sun biwo bayan wanda su ka wakana jiya lahadi, inda yan yaƙin sari ka noƙe, su ka bingide, har lahira yan sunni 42.

Sannan a sassa daban daban na kasar, yan kunar bakin waken,sun kai hare hare masu yawa, a tsukin yan kwanaki 2.

A ɗaya hannun, kuma, yau ne, a ka koma sauraraen shari´ar tsofan shugaban ƙasa Saddam Hussain.

Saidai lauyoyin Saddam Hussain, sun ƙauracewa wannan shari´a, su na bukatar samun cikkakar kariya, da kuma bunɗa bincike, a kan mutuwar ɗaya daga lauyoyin da a ka hallaka a watan juni da ya gabata.