1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran adawa ya zama sabon shugababn

Abdourahamane Hassane
August 16, 2021

Hukumar kula da zabe a Kasar Zambiya ta sanar da cewar jagoran 'yan adawa Hakainde Hichilema ya samu nasara da gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasar da aka yi a makon jiya a gaban shugaba mai barin gado Edgar Lungu.

https://p.dw.com/p/3z23F
Sambia Luska | Oppositionskandidat | Hakainde Hichilema
Sabon shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema Hoto: Salim Dawood/AFP/Getty Images

Hakainde Hichilema dan shekaru 59 sau uku yana karawa da Shugaba Edgar Lungu a zaben shugaban kasar, sai a wannan jikon ya samu nasara a zaben wanda aka gudanar da shi a makon jiya, tun farko an yi ta hasashen cewar Edgar Lungu zai fadi a zaben saboda matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi. Jamiyyar PF da ke mulki ta Edgar Lungu ta ce tana nazarin shigar da kara domin kalubalantar sakamakon zaben  a gaban kotu.