Haider al-Abadi ya zama sabon firaministan Iraki | Labarai | DW | 11.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haider al-Abadi ya zama sabon firaministan Iraki

Babbar jam'iyyar kawance gwamnatin Iraki ta amince da sabon firaminista

Babbar jamiyyar mabiya Shia a Iraki sun zabi Haider al-Abadi tshohon ministan harkokin sadarwa a kasar, dan ya zama sabon Firemiya a kasar.

Kafar yada labarai ta Al-Forat ta bayyana a cikin rahoton data fitar cewa 127 daga cikin 173 na mambobin majalisar daga bangaren 'yan Shia sun bayyana goyon bayansu ga al-Abadi, duk kuwa da kafewar da al-Malikin ke yi na kafa sabuwar gwamnatin da kansa. Hakan na nufin cewa rabin mambobin jamiyyar sun kaurace wa al-Malikin.Tuni dai shugaba Fuad Masum ya bukaci mataimakin kakakin majalisa na farko Haidar al-Abadi da ya gaggauta kafa gwamnati, wannan kira kuwa na zuwane cikin wani kwarya-kwaryar biki da aka watsa ta kafar talabijin ta kasar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo