Haftar ya hana jiragen ruwa shiga Libiya | Labarai | DW | 03.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haftar ya hana jiragen ruwa shiga Libiya

Janar din nan Libiya da ke da karfin fada a ji wato Khalifa Haftar ya umarci sojin da ke biyayya gare shi da su hana duk wani jirgin ruwa na kasashen waje shiga kasar ta Libiya.

Mai magana yawun haftar din ne ya ambata hakan inda ya ce tuni shugaban rundunar sojin ruwan kasar da ke karkashin ikosa ya karbi wannan umarni na hana duk wani jirgi shiga kasar har sai ya samu izini daga gare shi. Wannan umarni na Khalifa Haftar ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin Italiya ta yi na aikewa da jami'anta domin hana amfani da gabar ruwa Libiya din don kaiwa ga tekun Bahar Rum da nufin isa Turai. Masu aiko da rahotanni suka ce daukar wannan mataki da Italiya ta yi tare hadin gwiwar mahukuntan Tripoli ka iya zama dalili na umarnin da Janar Haftar ya bada na hana jiragen kasashe shiga kasar kasancewar ba ya shiri da mahukuntan Tripoli din.