1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane shida sun mutu a Libiya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 1, 2022

Akalla mutane shida ne suka gamu da ajalinsu wasu fiye da 50 suka jikkata, sakamakon fashewar wata tankar mai a yankin Bent Bayyah da ke kudancin Libiya.

https://p.dw.com/p/4Ey43
Libyen Tripolis Explosionen Treibstofflager Flughafen 02.08.2014
Hoto: Reuters

Hatsarin ya faru ne a yayin da mazauna yankin suka yi dandazo kan tankar man don dibar ganima, lamarin da ya haifar da gobarar wasu karin motocin da ke ajiye a kusa da wurin da fashewar ta auku.

Tuni shugaban gwamnatin rikon kasar da ke birnin Tripoli Abdelhamid Dbeibah, ya nuna kaduwa kan hatsarin, tare da bayyana cewa gwamnatin tarayya na bin lamarin sau da kafa. 

Tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibitin da ke birnin Sabha, mai tazarar kilomita fiye da 700 daga birnin Tripoli don yi musu magani.