1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun mutu a hadarin mota

Abdoulaye Mamane Amadou Sulaiman Babayo
November 12, 2022

Ma'aikatar lafiya a Masar ta tabbatar da mutuwar mutane da dama, sakamakon hadarin wata motar safa a yankin Kogin Nilu na arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4JQnH
Ägypten Bus Unfall Urlaubsort Hurghada Hurgada
Hoto: Reuters

Wata motar safa da ta yi hadari a yankin arewacin Masar ta zama sanadiyar mutuwar mutane 19 a wannan Asabar. Jami'an agaji sun ce hadarin da ya auku a yankin kogin Nuli ya kuma raunata mutane shida da ke samun kulawar likita.

Kimanin mutane 7000 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon haduran motoci a kasar masar a shekarar 2021, duk da yake Masar na zama kasa mafi yawan al'umma a daukacin kasaashen yankin Larabawa. Ana zargin lalacewar hanyoyi a cikin wasu dalilan da ke haddasa yawan hadurran motocin da sauran ababen hawa a kasar Masar.