Hadarin jirgin kasa a Engla | Labarai | DW | 24.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadarin jirgin kasa a Engla

Akalla mutun daya ya mutu, yayin da wasu mutane dari suka samu raunuka, a wani hadarin jirgin kasa da ya auku a arewacin Ingila. Ma’aikatan agaji, sunce har yanzu dai ana cigaba da kokarin fitar da wasu mutane da yawa da jirgin ya fada kann su. Rahotanni sun tabbatar da cewar akalla mutane 8 na cikin halin kaka ni-ka-yi, bayan wasu uku dake nan rai Allah. Hadarin ya auku ne lokacin da jirgin, mai tafiyar saurin kilo-mita 180 cikin awa daya, bayan ya tashi daga birnin London zuwa Glasgow, ya saki hanyar sa, ya fada wasu ramuka.