1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum 6 sun mutu a hadarin jirgin sama

Ramatu Garba Baba
December 9, 2018

Manyan jami'an gwamnati shida ne suka mutu a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya auku a wannan Lahadin.

https://p.dw.com/p/39lPB
Sudan Flugzeugabsturz
Hoto: Getty Images

 A sanarwar da mahukuntan Sudan suka fitar bayan aukuwar lamarin , sun ce akwai gwamna guda da kuma ministan ma'aikatar noma daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin. Wasu shedun gani da ido sun ce jirgin ya kama da wuta bayan da ya daki wani karfe inda daga bisani ya fado kasa. Lamarin ya auku a wani yanki da ke a gabashin kasar.