1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgi ya halaka rayuka a Pakistan

May 22, 2020

Rahotanni daga Pakistan na cewa wani jirgin sama da ke dauke da sama da mutum 100 ya yi hadari a wani rukunin gidaje a kudancin Karachi babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3cdYo
Symbolbild Pakistan Absturz eines Flugzeuges in Karachi
Hoto: AFP/F. Naeem

Bayanai sun ce jirgin ya taso ne daga birnin Lahore da ke gabashin kasar ta Pakistan, wanda kuma ya kife 'yan dakikoki kalilan kafin ya sauka a Karachi. Mai magana da yawun gwamnatin lardin, Abdul Rashid Channa, ya tabbatar da rasuwar kusan dukkanin fasinjojin jirgin, in banda wani mutum daya da ya tsira amma yana kan karbar magani a asibiti. 

Tun da fari dai, wata majiyar sojin kasar da ke ayyukan bayar da agajin gaggawa a inda abin ya faru, ta bayyana cewa sun samu mutane 15 da suka jikkata kuma tuni aka kai su babban asibitin kasar domin yi masu magani wadanda daga bisani suka ce ga garinku nan. Kasar ta Pakistan dai ta fara sufurin jiragen samanta a cikin gida tun 15 ga watan nan da muke ciki na Mayu bayan dage dokar kulle da ta yi.