Habasha: Kura ta fara lafawa | Siyasa | DW | 25.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Habasha: Kura ta fara lafawa

Al'amura sun daidaita bayan juyin mulkin da aka yi yunkurin yi a ranar Asabar din da ta gabata amma masharhanta na cewar yunkurin zai taimaka wajen dagula lamuran siyasa.

Gwamnatin kasar ta Habasha dai ta bayyana cewar galibin wandada ake zargi da hannu kan juyin mulkin na ranar Asabar mutane da suka yi kaurin suna wajen tada rikici a kasar, to amma tuni suka shiga hannu inji mahukunta na Addis Ababa. Wani abu har yau shi ne irin matakan da suka ce sun dauka wajen ganin hankula sun kwanta domin a samu cigaba da hidimomin yau da kullum.

Äthiopien Trauerfeier für General Seare Mekonnen (picture-alliance/AP Photo/M. Ayene)

Aby Ahmed a yayin jana'izar sojojin da suka mutu a lokacin gumurzun kwace iko

To sai dai duk da wannan mataki da hukumomin suka ce sun dauka da ma irin kokarin da Firaiministan ya yi na sakin fursunonin siyasa da kuma janye haramcin da ya yi kan wasu kungiyoyi na 'yan adawa, masharhanta kan lamuran siyasa na kasa da kasa irin su Dr. Annette Weber na ganin tun da fari gwamnatin Abiy Ahmed ba ta tsayin daka ba sosai wajen ganin rikicin kabilancin da kasar ke fuskanta da kuma irin abin da ya faru ranar Asabar din bai faru ba.

Yanzu haka da dama na zuba idanu don ganin yadda lamura za su kasance a kasar ta Habasha da ma irin matakan da  Firaiministan da ya yi fice wajen ganin ya sansanta bangororin da ke rikici musamman ma a wasu kasashen Afirka zai dauka wajen wanzar da zaman lafiya a kasar wanda kan wani bangare na al'ummarta ke a rarrabe.

Sauti da bidiyo akan labarin