1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi mace shugabar kasar Habasha

October 25, 2018

'Yan majalisar dokokin Habasha sun zabi mace ta farko Sahle-Work Zewde a matsayin shugabar kasa a dai dai lokacin da kasar ke fama da rikice-rikicen kabilanci.

https://p.dw.com/p/37DHZ
Äthiopien Addis Abeba neue Präsidentin Sahle-Work Zewde
Hoto: Getty Images/AFP/E. Soteras

A wani zaben da ‘yan majalisar ta Habasha suka yi a wannan Alhamis ne suka tabbatar da Sahle-Work Zewde ‘yar shekaru 68 a matsayin shugabar kasa, kasar da ke zama ta biyu mafi yawan al’uma a Afirka.

Nadin nata ya zo ne bayan murabus din da Mulatu Teshome wanda ke matsayin ya yi, ba tare da yin wani karin bayani ba. A makon jiya ne dai firaministan kasar Abiy Ahmed, da ake yi wa kirari da mai akidar sauyi, ya nada mata kashi 50% na ministocin kasar, ciki har da mukamin ministar tsaro. Wasu daga cikin ‘yan kasar dai sun yaba matakin, musamman wadanda ke da’awar tafiya da zamani ta hanyar jingine wasu tsare-tsaren da ke da ake dangantawa da al’ada.

Äthiopien Addis Abeba neue Präsidentin Sahle-Work Zewde
Majalisar dokokin kasar HabashaHoto: Getty Images/AFP/E. Soteras

Ita dai madam Sahle-Work Zewde, da aka haifa a Addis Ababa babban birnin kasar, ta yi karatunta na jami’a ne a kasar Faransa, kuma ta taba yin aikin jakada a kasashen Faransa da Djibouti da Senegal ta kuma rike mukami a kungiyar raya ci gaban kasashen gabashin Afirka. Gabanin wannan nadin babbar jami’a ce a kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Yanzu dai a bisa tsari, za ta rike sabon mukamin nata ne na tsawon shekaru shida har sau biyu. Shugabancin kasar dai galibi ofishin firamnista ne ke gudanar da shi, yayin da shugaban kasa kuma ke maida hankali ga wasu muhimman bukukuwa da ake yi a kasar.