Gwamnatin wuncin gadin kasar Libiya ta yi murabus
August 29, 2014Talla
Gwamnatin wucin gadin kasar Libiya ta bayyana murabus bayan masu kaifin kishin addinin Islama sun kirkiro wata gwamnati. A daren wannan Alhamis da ta gabata jagoran gwamnatin wucin gadin Firaminista Abdullah al-Thani ya shaida wa majalisar dokokin murabus da gwamnati ta yi.
Saboda dalilan tsaro majalisar tana zama a garin Tobruk mai nisan kilo-mita 600 daga Tripoli babban birnin kasar. Wannan murabus da gwamnatin Libiya ta yi ya zo kwanaki uku, bayan tsohuwar majalisar dokoki ta zabi mai kishin Islama Omar al-Hassi a matsayin sabon firamnista.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman