1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin albashin ma'aikatan gwamnati

Binta Aliyu Zurmi
May 14, 2022

Mahukunta a Tanzaniya sun sanar da karin albashi ga ma'aikatan gwamnati matakin da ake gani zai rage wa al'umma radadin tsadar rayuwa da ake ciki.

https://p.dw.com/p/4BJPH
EAC Staaten Video-Konferenz | Samia Suluhu Hassan
Hoto: Philbert Rweyemamu/EAC

Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta amince da karin mafi karancin albashi da kaso 25 cikin dari, wannan karin na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar kasar ke fama da matsin tattalin arziki.

Ko baya ga wannan karin Shugaba Samia kazalika ta sanar da kara albashin ma'aikatan gwamnati, wanda ke zama karon farko tun daga shekarar 2016.

Tun bayan darewa karagar mulki a shekarar da ta gabata bayan mutuwar Shugaba John Magufuli, sannu a hankali shugabar Tanzaniyar kuma mace ta farko kan wannan mukami, ta fara sauya akalar gudanarwar gwamnatin marigayin.