Gwamnatin Saudiya zata tattauna da Iran | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Saudiya zata tattauna da Iran

Jakadan kasar saudiya a kasar Amurka yace,Saudiya tana shirin tattaunawa da kasar Iran game da aiyukanta na nukiliya.

Yarima Turki al-Faisal,ya baiyanawa majalisa mai kula da hulda da kasashen wajen Amurka,a lokacinda ta tambayae shi game da batun lakabawa Iran takunkumi,jakadan yace ba zai ce komai ba game da wannan batu,saboda kasarsa tana shirin tattaunawa da Iran game da harkokinta na nukiliya.

Yarima faisal ya kuma baiyanawa majalisar cewa, musulmi da dama sunji takaicin harin ranar 11 ga watan satumba da hare hare da ake ci gaba da kaiwa a kasar Iraqi.