Gwamnatin Libiya ta kwace birnin Sirte | Labarai | DW | 18.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Libiya ta kwace birnin Sirte

Gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan kasashen duniya ta bayyana nasarar sake kwace birnin Sirte daga tsagerun IS.

Gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan kasashen duniya ta bayyana samun nasarar kwace birnin Sirte daga hannun mayakan kungiyar IS masu ikirarin neman kafa daular Islama. Firamnistan gwamnatin Fayez Serraj ya bayyana haka yayin jawabi ta tashar talabijin.

Makonni biyu da suka gabata gwamnatin ta tabbatar da kwace galibin sassan birnin daga hannun 'yan IS, inda 'yan kungiyar ke dauka a matsayin shalkwatarsu. Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka ta fada rudanin siyasa da tattalin arziki tun shekara ta 2011, sakamakon boren juyin juya hali da ya kai ga kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.