Gwamnatin Libiya ta janye daga tattaunawa da ′yan tawaye | Labarai | DW | 23.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Libiya ta janye daga tattaunawa da 'yan tawaye

Majalisar dokokin kasar da duniya ta amince da ita ta kada kuri'ar dakatar da hawa kan teburin sulhun da masu ta da kayar baya.

Gwamnatin Libiya ta sanar da dakatar da shiga tattaunawar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya domin shiga tsakanin mahukuntan na Libiya da 'yan tawayen kasar. Majalisar dokokin kasar da duniya ta amince da ita ce a wannan Litinin ta kada kuri'ar dakatar da shiga cikin tattaunawar a dai-dai lokacin da ake shirin shiga sabon zubi na hawa kan teburin sulhun a kasar Moroko a ranar Alhamis mai zuwa. Daya daga cikin mambobin majalisar Issa al-Aribi ya bayyana batun dakatar da shiga tattaunawar na bangaren gwamnatin ta Libiya a shafinsa na Facebook. Sai dai bai yi karin haske a kan dalilin da ya sanya suka dakatar da zama kan teburin sulhun ba. Amma tuni shafin sada zumunta na Facebook na kamfanin dillancin labaran kasar da kuma na majalisar dokokin kasar suka tabbatar da batun dakatar da shiga tataunaar da 'yan tawayen kasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourrahmane Hassane