1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kamaru ta fara yaki da masu safarar ma'adinai

Zakari Sadou AH
March 18, 2026

Shugaba Paul Biya ya umurci da aka kafa kwamitin hadin gwiwa cikin gaggawa da zai yi bincike don yaki da masu safarar zinari ba bisa kaida ba.

https://p.dw.com/p/5Ac7c
Masu hakar zinari ba bisa kaida ba a Kamaru
Masu hakar zinari ba bisa kaida ba a KamaruHoto: Elisabeth Asen/DW

Domin gudanar da wannan binciken, an tura jami'an tsaron kasa nan take wuraren hakar ma'adinai da ke yankin gabashin kasar don bankado masu hannu a safarar zinarin kasar ba bisa ka'ida ba, kawo yanzu rahoton ya nuna cewa kilogram 953 na zinarin kasar kacal aka fitar a rahoton gwamnatin wannan rahoto ya sabawa binciken da ya nuna cewa zinarin da aka fitar ya ninka  sau 600 akan zinarin da aka fitar ba bisa ka'ida ba.

Paul Biya
Paul Biya Hoto: Jacovides Dominique/Pool/ABACA/picture alliance

Dr Bareja Youmssi masanin ilimin karkashin kasa ya daura laifin a kan  gwamnatin kasar "Kusan ayyukan Kamaru ne ke bi ta hanyar da ba su dace ba, ku yi tunani ku gani tan 15 shi ne tan dubu 15 kwatankwacin CFA biliyan 900.''

Wannan asarar kudin shiga da Kamaru ke yi yawancin lokaci na da alaka da rashin kishin kasa ga wadanda shugaban kasar ke nadawa duba sama da fadi da ake yi da dukiyar kasar wanda yana daya daga cikin al'amuran da suka lalata tattalin arzikin kasar har yana kai wa a ciwo bashi don wasu ayyukan kasar.