Gwamnati Zambiya ta cafke ′yan jarida | Labarai | DW | 28.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnati Zambiya ta cafke 'yan jarida

Mutane uku da gwamnati Zambiya ta cafke sun hada da 'yan jarida biyu bayan rufe jadiyar Post.

'Yan sanda a kasar Zambiya sun tuhumi muitane uku da suka hada da 'yan jarida biyu, wadanda aka rufe gidan jaridar da suke aiki saboda sun shiga gidan jaridar da aka rufe. Jaridar ta kasance mai sukar gwamnatin kasar, yayin da ake kara zaman zullumi bisa zaben kasa baki daya na watan Agusta mai zuwa.

Hukumar tara kudaden shiga ta rufe jaridar Post a makon jiya saboda rashin biyan kudaden haraji na dala milyan shida, amma jaridar ta zargi gwamnatin ta Zambiya da neman rufe bakin masu adawa da ita, sannan ta kara da cewa dokar ta aka yi aiki da ita tana gaban kotu, saboda akwai takaddama.

Tuni Shugaba Edgar Lungu na kasar ta Zambiya ya kare matakin hukumar tara kudaden shigar. 'Yan jarida suna zargin gwamnati ta dauki matakin domin rufe bakin masu adawa da ita.