1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati ta tsaurara tsaro a Mali

March 26, 2019

Rikicin kabilanci a kasar Mali ya tilasta hukumomin kasar tsara sabbin dabarun murkushe tashe-tashen hankula da ke sanadiyyar rayukan jama'a da kadarori.

https://p.dw.com/p/3Fet3
Mali Soldat der Armee
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Maeterlinck

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na kasar ta Mali, ya yi alkawarin daukar matakan tsaro da suka dace a yankunan da ake samun tashe tashen hankula. Hakan dai na zuwa ne bayan wasu kabilu sun afka wa al'umar fulani a wani kauye inda suka kashe sama da mutum 130.

Yayin wata ziyarar da ya kai kauyen Ogassogou da abin ya faru, Shugaba Keita ya bai wa hafsan hafsoshin kasar Janar Aboulaye Coulibaly izinin yin abin da ya dace, yana mai jaddada cewar dole ne a yi adalci.

Shugaban na Mali dai ya nada Janar Coulibaly ne, bayan kisan da aka yi wa fulanin a kauyen da ke a tsakiyar kasar ranar Asabar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ce baya ga kisan mutanen, an ma kona gidajensu da sauran kadarorin da suka mallaka.