Gwamnati ta ce sun amince da tsagaita wuta da Boko Haram | Labarai | DW | 17.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnati ta ce sun amince da tsagaita wuta da Boko Haram

Labarin cimma yarjejeniyar dai na zuwa ne dai dai lokacin da shugaban Najeriya ke daf da bayyana matsayinsa a sake tsayawa takaran zaben badi.

Rahotanni da suka fito daga bakin jami'an gwamnatin Najeriya, sun suka ce wai ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Kungiyar Boko Haram da batun sako yaran nan 'yan makarantar Chibok sama da dari biyu da kungiyar mayaƙan na Boko Haram ta sace sama da watanni shida.

Sai dai fa wadannan bayanan sun fito ne daga wasu majiyoyi na fadar shugaban ƙasa. Inda suka ce ya zuwa yanzu batutuwa biyu aka cimma ƙarƙashin wannan yarjejeniya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya shaidar, sune ɓangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta sannan za a sako yaran nan na Chibok da aka kama a makarantarsu da ke a arewa maso gabashin Najeriya.