Gwamnati da yan tawaye na Nepal sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya | Labarai | DW | 21.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnati da yan tawaye na Nepal sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Gwamnatin mai jamiyu da yawa ta kasar Nepal tare da yan tawayen Mao sun rattaba hannu kann wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka shirya da nufin kawo karshen shekaru 10 na tawaye wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 13,000.

Karkashin yarjejeniyar,yan tawayen zasu shiga gwamnatin rikon kwarya ta kasar,su kuma mika makamansu tare da kasancewa a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya kafin zaben kasar da zaa gudanar a shekara mai zuwa.

An cimma wannan yarjejeniyar ce watanni 7 bayan sarki Gyanendra ya mika mulki ga jamiyun siyasa na kasar,biyowa bayan tarzoma na makonni da akayi na adawa da mulkinsa.

Yan tawayen dai suna kokarin ganin an soke masarautar kasar ta Nepal.

A yanzu haka dai sunyi alkawarin mutunta sakamakon zabe a kasar.