1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamman bakin haure sun nutse a teku

Binta Aliyu Zurmi
February 15, 2023

Wani jirgin kwale-kwale makare da 'yan gudun hijira da ya taso daga gabar tekun Libiya ya nutse, inda sama da mutane 70 suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/4NXW5
Lebanese forces rescue about 200 migrants after boat sinks
Hoto: Lebanese Army/AP/picture alliance

Daga cikin mutane 80 da jirgin ya kwaso, 73 sun bace inda ake zaton ko sun mutu. An dai sami gawar mutum 11 daga cikin su da suka hada da gawar mace guda.

Hukumar kula da kaurar jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ta ce wanann mumunan hadarin ya auku ne a jiya Talata yayin da mutanen ke hanyarsu ta zuwa Turai domin samun kyakyawar rayuwa.

Masu tsaron gabar teku sun yi nasarar ceto mutum 7 a raye wadanda dukkaninsu maza ne, kuma tuni aka garzaya da su asibiti don basu kulawa ta gagawa.

Yin kaura ta barauniyar hanya zuwa nahiyar Turai ta jima tana jawo hasarar rayukan dubban mutane, wanda kasashen yamma ke kokarin ganin an kawo karshen shi.