Guterres: Barazanar tsaro na karuwa a Mali
March 6, 2019Talla
Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya Antonio Guterres, na cewa barazanar 'yan bindigar da ke sheke aya a Mali na ci gaba da yaduwa ne musamman daga yankin tsakiya zuwa arewacinta.
Hakan kuwa a cewarsa na matukar durkusar da kokarin da ake yi na ganin an cimma yarjejeniya ta zaman lafiya da su masu tayar da kayar bayan.
Cikin wannan watan ne dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar ke shirye-shiryen kai ziyara kasar ta Mali, dangane da yiwuwar tsawaita wa'adin zaman dakarun kiyaye zaman lafiya na MINUSMA da ke can.