Guido Westerwelle tsohon ministan harkokin wajen Jamus ya rasu | Labarai | DW | 18.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guido Westerwelle tsohon ministan harkokin wajen Jamus ya rasu

Tsohon ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Guido Westerwelle da ke daya daga cikin futattun 'yan siyasar kasar daya bayyana kansa a matsayin mai neman maza ya rasu a ranar juma'ar nan.

Guido Westerwelle mai shekaru 54 a duniya wanda ya rasu a Cologne a ta cewar cibiyar Westerwelle mai bayar da agajin jin kai, a inda ta kara da cewar tsohon ministan ya dade yana fama da cutar tun a shekara ta 2014.

Dan siyasar wanda yayi hannun riga da harkokin siyasa a shekara ta 2013 bayan da jam'iyyar sa ta Liberal da FDP sun rasa kujeru a majalisar dokokin Jamus.

Kazalika tsohon minisatan harkokin wajen Jamus din Guido Westerwelle ya kuma jagoranci jam'iyyar FDP tun daga shekara ta 2001 zuwa 2011 kana kuma ya rike mukamin ministan harkokin wajen Jamus a karkashin gwamnatin Angela Merkel daga shekara ta 2009 zuwa 2013.