Guguwar Milton ta isa gabar ruwan Florida
October 10, 2024Talla
Iftila'in ya haifar da ambaliyar ruwa da kuma daukewar wutan lantarki. Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi kira ga mazauna Florida da su mutunta dokar kwashe jama'a daga yankin, yana mai cewa ta yiwu guguwar ta Milton ta kasance iftila'i mafi muni da jihar za ta fuskanta cikin shekaru 100.
Karin bayani: Guguwa ta sa Joe Biden dage ziyararsa zuwa Jamus da Angola
Kawo yanzu dai fiye da mutane miliyan daya ne ke zaune a cikin duhu yayin da ake ci gaba da gargadin mutane kan walkiya da ma ambaliyar ruwa a yankin Tampa. Ana sa ran guguwar ta ratsa zuwa gabar tekun Florida daga Yamma zuwa Gabas yayin da take rage tasiri, sai dai har yanzu tana ci gaba da zama barazana.