Guguwar Haiyan ta haddasa mummunar ɓarnar a Philippine da Somaliya | Zamantakewa | DW | 14.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Guguwar Haiyan ta haddasa mummunar ɓarnar a Philippine da Somaliya

Kusan mutane dubu 2500 suka rasa rayukansu a Philippine yayin da wasu 300 suka mutu a yankin Puntland na Somaliya a sakamakon kaɗawar guguwar Haiyan da ta ratsa yankuna daban-daban.

Tun a makon jiya ne mahaukaciyar guguwar nan da ake kira da sunnan Haiyan haɗe da iska mai ƙarfin gaske da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ta afka wa wasu yankunan da ke a gaɓar tekun Philipine,inda ta yi kaca-kaca da gidaje tare da tsinke layukan tarho da na wutar lantarki. Guguwar dai ta fi ɓarna a Tacloban inda dubban jama'a suke cikin wani mawuyacin hali. Sannan kuma guguwar ta bazu har yazuwa Somaliya inda a can ma ta yi mummunar ɓarna. Saboda haka ne muka yi muku tanadin rahotannin waɗanda ke a ƙasa jere.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin