Hasashen masana kan sauyin yanayi | Siyasa | DW | 12.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hasashen masana kan sauyin yanayi

Bala'in iska mai ƙarfi wanda aka dangata da samun asali bisa sauyin yanayi, ya yi mummunar ɓarna a ƙasar Phillipines abinda kuma ya jawo mahawara tsakanin masana

Maukaciyar guguwar da yanzu haka ke kaɗawa a yankin Asiya, wanda kuma ta yi mummunar ɓarna a ƙasar Philippines, inda mutane da dama su ka mutu. Wannan guguwar mai ƙarfi, an ji kadawarta har a ƙasashen gabashin Afirka da ke gaɓar Tekun Indiya, kamar misali ƙasar Somaliya. Masana sun bayyana cewa babban dalilin irin wannan mahaukaciyar guguwa shi ne, sauyin yanayi.

A fadar masanin kimiyar yanayi da ke ƙasar Jamus, Christian Herold, ya ce a shekarun da suka gabata babu wani babban mataki na bin tsarin da aka yi, bisa sauyin yanayi, inda aka mai da hankali kawai bisa bayanan da taurraun ɗan Adam ke bayarwa.

Residents wade through a flooded street outside a traffic police station after rainstorms triggered by Typhoon Haiyan hit Sanya, Hainan province November 11, 2013. Rainstorms from the typhoon hit the south China region on Sunday and Monday, killing at least four, with seven people still missing, according to Xinhua News Agency. Haiyan, one of the most powerful storms ever recorded, killed an estimated 10,000 people in central Philippines, according to officials. Picture taken November 11, 2013. REUTERS/China Daily (CHINA - Tags: ENVIRONMENT DISASTER SOCIETY CRIME LAW) CHINA OUT. NO COMMERCIAL OR EDITORIAL SALES IN CHINA

Guguwar Taifun Haiyan a China

"Ba'a bi diddigin lamarin yadda ya kamata ba, don haka binciken da aka gudanar ya yi kaɗan. A 'yan shekarun da suka gabata mun fara yin amfani da taurarun ɗan Adam"

Mahaukaciyar guguwa kamar ta Horricane, Taifun da dai sauransu, irin waɗannan bala'o'i da ake samu a yancin hamada suna matuƙar buƙatar binciken masana da gwaji ɗaya izuwa sau biyar. Masana suka ce idan an yi bincike mai zurfi kamar haka ne, za su iya sanin ta ina iskar za ta taso, kana ina da ina za ta shafa, kana su na iya yin ƙiyasin ɓarnar da za ta iya haddasawa. Friedrich Wilhem Gersterngarbe da ke cibiyar kula da mahalli a Postadam a ƙasar jamus ya yi ƙarin haske.

epa03946097 A Filipino soldier secures a child from the crowd prior to boarding a military C-130 plane at the airport of the super typhoon devastated city of Tacloban, Leyte province, Philippines, 12 November 2013. Aid workers and relief supplies were being poured into eastern provinces hit by Typhoon Haiyan, which aid agencies and officials estimated has left thousands dead and staggering destruction in its wake. The United States will send an aircraft carrier and other Navy ships along with 20 million dollars in emergency humanitarian aid to the Philippines. Thousands were feared dead in Leyte and nearby Samar province, as police and disaster relief officials said at least 552 were confirmed killed, mostly drowned by tsunami-like sea waves that flattened towns. EPA/DENNIS M. SABANGAN

Waɗanda bala'i ya shafa a Philippinen

"Irin wannan mahaukaciyar guguwa da ke kaɗawa a Phillipines yanzu haka, a ƙashin gaskiya ba mu maida hankali a kanta b, inda ta ke gudun kilo mita 300 a sa'a guda. Gudun iskar abu gudane, sannan kuma guguwar ta haddasa ambaliyar dama-damai da koguna. Akwai mummunar ɓarna da ambaliya ta yi"

Masana daban-daban dai sun sha bayana cewa, bincikensu ya nuna alamar samun ƙaruwar sauyin yanayi, wanda kuma a 'yan shakarunnan aka ga yadda yake haddasa bala'o'i a ƙasashen duniya, musamman waɗanda ke gaɓar ruwayen teku.

"Akwai yankuna da dama, waɗanda zafin ruwan tekunansu ya ƙaru. Ciki harda yankin Karibiyan, inda wannan guguwar Taifun ta faro. A wannan yankin zafin ruwayen tekunansu yakan kai maki 30 a ma'aunin zafi. A da kuwa bai wuce maki 27 izuwa maki 28"

A slogan is projected by Greenpeace activists on a cooling tower of Belchatow Power Station, Europe's largest coal-fired power plant, in Belchatow November 9, 2013. The 19th conference of the United Nations Framework Convention on Climate Change will begin in Warsaw from Monday, November 11. Picture taken on November 9, 2013. REUTERS/Tomasz Stanczak/Agencja Gazeta (POLAND - Tags: ENERGY BUSINESS ENVIRONMENT CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY) ATTENTION EDITORS - THIS IMAGE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. THIS PICTURE IS DISTRIBUTED EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS. POLAND OUT. NO COMMERCIAL OR EDITORIAL SALES IN POLAND. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS

Yahaƙi masu gurɓata mahalli da ga masana'antu

Wata babbar matsala da ta fi kasance wa masanan kimiyar yanayi gagara badau shi ne, yadda ba da safai su ke iya sanin haƙiƙanin wace irin iska za a yi ba, kuma wane irin nau'in za ta bullo ba. Don haka ko da sun yi bincike, sau tari akan samu bala'in da ke aukuwa ya saɓa da tunaninsu.

Yanzu dai abin da ya ragewa gwamnatocin duniya shi ne, shin ko za su ɗau ƙwararan matakai na kare mahalli, ta inda za a tsawatar wa masana'antu wajen rage fidda hayaƙi masu sa guba?. Ko kuma duniya ta ci gaba da kasan cewa cikin hatsari na aukuwar bal'a'o'i, waɗanda ke samun asali daga sauyin yanyi.

Mawallafa: Brigitte Osterath/ Usman Shehu Usman
Edita: Pinado Abdu

Sauti da bidiyo akan labarin