1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Gudunmawar Musulmi Bakar fata

Mahmud Yaya Azare LMJ
October 6, 2020

Cibiyar kyautata fahimta tsakanin mabanbamta addinai da ke birnin Santambul na Turkiya, ta shirya taron bita kan irin rawar da Musulmi bakaken fata ke takawa kan koyarwar Musulumci.

https://p.dw.com/p/3jVLs
Türkei Istanbul | Moschee wird zur Hilfsstation für Betroffene der Coronakrise
Hoto: DW/S. Rahim

Wannan taron dai, ana gudanar da shi ne kai tsaye ta hanyar internet, inda ake gabatar da bayanai daga bakin masana da kuma malamai dangane da irin kokarin da bakaken fata Musulmin suka yi kuma suke kan yi a bangarori dabam-dabam na ci-gaban al'umma, daga ciki kuwa har da irin yadda Musulmi bakaken fatar suka taka rawa tare da bayar da gudunmawa wajen yada ilimin addinin  Islama.

Sau tari dai a kan samu bakaken fata ne suka fi karbar addinin Musluci a cikin kasashen Turai. Babbar manufar wannan taro dai ita ce kara karfafa wa bakaken fata Musulmi gwiwa domin ci gaba da kokarin da suke yi a bangarori dabam-dabam, duk kuwa da irin matsalolin da suke fuskanta.