1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Grace Mugabe ta fadi shari'a kan lu'u-lu'u

Mouhamadou Awal Balarabe
December 22, 2016

Uwargidan shugaban Zimbabuwe zata mayar da kadarorin wani dan kasuwa da ke hannunta bisa umurnin kotu bayan data fadi shari'ar da take yi da wani dan kasuwa kan zoben lu'u-lu'u.

https://p.dw.com/p/2UlGq
Grace Mugabe
Hoto: J. Njikizana/AFP/Getty Images

Kotun kasar Zimbabuwe ta umurci matar shugaba kasa Robert Mugabe da ta maida ma wani dan kasuwa duk kadarorinsa da ta rike sakamkon rikici da ya hadasu kan wani zoben lu'u-lu'u wanda darajarsa ya kai miliyan guda da dubu 35 na Dollar. Ita dai Grace Mugabe ta ki karbar zoben da ta yi oda, tare da neman a biyata kudinta nan take.

Duk wani yunkuri da dan kasuwa Jamal Ahmed ya yi na biyanta kudinta daki-daki ya ci tura, lamarin da ya sa baya ga barazana daga jami'an tsaro, Grace mugabe ta kame wasu daga cikin benayen da ya mallaka: Sai dai kotu ta cematakin  ya saba wa dokokin cinikayya.

Fadar shugaba Mugabe ba tace uffan ba tukuna dangane da wannan hukunci. Sai dai an saba ambato sunan Grace Mugabe a badakalar da ta shafi kayan kawa da kuma cin hanci da karbar rashawa. Sannan kuma an dade ana danganta Grace Mugbe da wacce zata iya maye gurbin maigidanta a takarar shugabancin Zimbabuwe. Ita ce ma yanzu haka take shugabantar reshen mata na jam'iyyar ZANU-PF da ke mulki.