Gobara ta yi ta′adi a Australiya | Labarai | DW | 14.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta yi ta'adi a Australiya

Rahotanni daga Melbourne na kasar Australiya na cewa wutar daji ta haddasa barna inda ake ta kokarin kaurar da mutane saboda girman lamarin. Akwai dai yiwuwar shawo kan gobarar ya debi tsawon kwanaki.

A Birnin Melbourn na kasar Australiya, masu aikin ceto da kashe gobara sun yi haramar kwashe daruruwan mutane daga gidajensu sakamakon barkewar wutar daji. Wutar dai ta soma ne tun safiyar jiya Alhamis kuma kawo i yanzu ana kokarin shawo kanta ba tare da an yi nasara ba.

Babu dai cikakken bayani kan asarar rai, sai dai mahukuntan kasar sun sanar da cewa aikin kashe wutar zai iya daukar kwanaki kafin a shawo kan lamarin baki daya, wannan shi ne karo na uku da ake samun aukuwar wutar daji a wannan yankin na kasar Australiya a shekara guda.