Gobara ta tashi a Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 26.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta tashi a Koriya ta Kudu

Mutane akalla guda 41 suka mutu kana wasu 80 suka jikkata a sakamakon gobarar a cikin wani asibitin mai hawan bene bakwai.

Masu aiko da rahotannin sun ce da dama daga cikin marasa lafiyar sun mutu a lokacin da ake kokarin cetonsu. Shugaban kasar na Koriya ta Kudu  Moon Jae-In  ya bayana takaicinsa a game da abin da ya faru kana kuma ya kira taron gaggawa na majalisar ministocinsa. Sai dai kuma kawo yanzu ba a san dalilan tashin wutar gobarar ba.