Gobara ta hallaka mutane 232 a Brazil | Labarai | DW | 27.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta hallaka mutane 232 a Brazil

Mahukuntan ƙasar Brazil sun ce aƙalla mutane 232 su ka hallaka sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan rawa

Mahukuntan ƙasar Brazil sun ce aƙalla mutane 232 su ka hallaka sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan rawa mai shaƙe da mutane a garin Santa Maria da ke yankin kudancin ƙasar. Akwai wasu mutane 131 da su ka samu raunuka.

Mafi yawan waɗanda abun ya ritsa da su ɗallibai ne, kuma ana kyautata zaton akwai kimanin mutane 2000, lokacin da wutar ta tashi, yayin da ake wasannin wuta, kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Shugaban ƙasar ta Brazil Dilma Rousseff ta katse halartar taron tsakanin ƙasashen Latin Amurka ta Turai da ke gudana a ƙasar Chile, domin zuwa garin na Santa Maria ta gani da idonta yadda ma'aikatan agaji ke ɗaukan mataki.

'Yan uwa da abokan arzikin mutanen da abun ya ritsa da su, sun hallara yayin da ake aikin fito da gawawakin waɗanda su ka hallaka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi