Gobara ta hallaka mutane 12 a London | Labarai | DW | 15.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta hallaka mutane 12 a London

Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 12 wasu da dama kuma sun jikkata a gobarar da ta tashi a wani bene mai hawa 24 a birnin London

A kasar Britaniya mutane akalla 12 ne aka tabbatar da mutuwarsu a gobarar da ta auku a wani dogon benen da ke yammacin birnin London, inda jami'an kwana-kwana 200 ke kokarin shawo kan gobarar a  kokarin ceto wasu da dama da suka makale.

Gobarar da ta fara kusan karfe daya na dare agogon GMT, ta kuma mamaye ilahirin ginin mai hawa 24, yanzu haka mutane kusan saba'in da aka yi nasarar kubutarwa daga gobarar ake bai wa kulawa a asibitocin kasar.

Shaidun gani da ido sun fadawa manema labarai cewa, sun yi ta jin yadda mutane ke kururuwar kiran kai musu dauki cikin ginin wanda ke dauke da gidaje sama da 100.

Hukumomin kasar dai ba su kai ga tantance musabbabin tashin wutar ba,sai dai sun kawar da fargabar da ake yi na cewa ginin na hasumiyan Greenfell zai iya rushewa.

Wuta na ci gaba da ci a ginin yayin da hukumomin kasar ke cewa za a iya daukar kwanaki kafin a shawo kan gobarar baki daya.