1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Gobara ta halaka mutane da dama a gidan wasan yara a Indiya

May 25, 2024

Kimanin mutane 24 suka mutu ciki har da kananan yara sakamakon tashin wata gobara a gidan wasan yara a jihar Gujarat da ke shiyyar yammacin kasar Indiya.

https://p.dw.com/p/4gHjH
Gidan wasan yara na Rajkot, a jihar Gujarat da ke Indiya da gobara ta halaka mutane da dama
Gidan wasan yara na Rajkot, a jihar Gujarat da ke Indiya da gobara ta halaka mutane da damaHoto: Str/REUTERS

Magajiyar Garin Nayana Pedhadiya, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa adadin mutanen ka iya zarta hakan, inda ta ce sun sha alwashin hukunta duk wanda ke da hannu a tashin gobarar.

Karin bayani: Indiya: Gobara ta kashe mutane 27 

Wasu hotunan da aka wallafa a kafar talabijin ya nuna yadda hayaki ya turnuke sararin samaniyar gidan wasan yaran a yammacin wannan rana ta asabar, inda gobarar ke ci gaba da tashi cikin gaggawa.

Karin bayani: Indiya: Gobara ta kashe masu jinyar corona

Firaiminstan Indiya Narendra Modi, ya ce gwamnati na ci gada da daukar matakan kula da wadanda ke da sauran numfashi a yayin hadarin tare kuma da nuna alhini kan iyalan da suka rasa 'yan uwansu sakamakon tashin gobarar.