Gobara a filin saukan jiragen saman Kenya | Labarai | DW | 07.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara a filin saukan jiragen saman Kenya

Mahukuntan Kenya na shirin sake bude filin jirgin birnin Nairobi da aka rufe saboda gobara.

Mahukuntan kasar Kenya sun ce, wani lokaci a wannan Laraba za a sake bude filin saukan jiragen saman Nairobi babban birnin kasar, wanda aka rufe sakamakon gobarar da ta tashi.

Kakakin shugaban kasar Manoah Esipisu ya baiwa masu zuba jari da matafiya tabbacin cewa, gwamnati tana iya bakin kokari domin sake bude zirga-zirga na cikin gida da kasashen duniya da kuma jigilar kayayyaki. Kuma gwamnati za ta bayyana lokacin da komai zai koma kamar yadda aka saba.

Gobarar da tashi ta janyo rufe daukacin harkokin yau da kullum a filin saukan jiragen saman na Nairobi babban birnin kasar ta Kenya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu