GMF: Hotunan bakin Sashen Hausa da suka halarci tarukan da suka gabata.
A ranaikun 14 da 15 ga watan Yuni ake gudanar da babban taron kafafan yada labaru na duniya wato Global Media Forum wanda DW ke shiryawa duk shekara. Ga hotunan bakin Sashen Hausa da suka halarci tarukan da suka gabata.
Tattaunawa da 'yan jarida da masana harkokin yada labaru
A babban taron kafafa yada labaru na Global Media Forum a shekarar 2019, makomar aikin jarida na cikin na daya daga cikin muhimmman batutuwan da aka duba. A hoton nan daga hagu zuwa dama: Michael Bröcker, babban edita na jaridar Rheinische Post, Jamus, Sa’a Ibrahim, shugabar Gidan Talabijin na ARTV, Kano Najeriya, Terry Martin na DW da Anna Minj, ta shirin karfafa aikin gamaiyyu, Bangladesh.
Taron GMF 2018: Ba da labarai kan ta'addanci
Marigayi Malam Umar Sa’id Tudun Wada, shugaban Gidan Rediyon Jihar Kano Najeriya. Ba da labarai kan ta'addanci: Waye ke ganin wani abu, yaushe kuma me ya sa? Wannan shi ne batun da marigayin ya yi tsokaci kai a taron GMF na 2018.
Lokacin musayar bayanai
A taron a kan samu wasu lokuta da manya da kananan 'yan jarida ke iya musayar bayanai, su dau hotuna da sauransu. A nan daga dama Ute Schaeffer, tsohuwar babbar editar DW da wakilinmu na Chadi Abdoulrazak Garba Baba Ani. sai kuma Matthias Wencke na DW (a baya).
Taron GMF 2018: Babban bako a Sashen Hausa
A lokacin taron GMF na 2018, Sashen Hausa na DW ya karbi bakoncin babban bako kuma tsohon shugaban Giadan Rediyon Kano Umar Sa'idu Tudunwada (a hagu), a tsakiya Zaharaddeen Umar da Malam Thomas Mösch.
Taron GMF 2017: Zanen barkwanci a matsayin makami
Abdulkareem Baba Aminu mai zanen barkwanci daga Najeriya a taron zanen barkwanci a atsayin makami a daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalia taron GMF na 2017. Abdulkareem Baba Aminu shi ke yi wa Sashen Hausa na DW zanen barkwanci da muke wallafawa a shafukanmu na intanet da sada zumunta.
Taron GMF na 2015
Tsohon ministan sadarwa na Jamhuriyar Nijar kuma tsohon ma'aikacin Sashen Hausa na DW, Yahouza Sadissou Madobi yana amsa tambaya kan kafar intanet a Afirka ko ci da gumin jama'a? A gefensa a hagu shugaban Sashen Hausa, Thomas Mösch.
Yahouza Sadissou da Peter Limbourg
Yahouza Sadissou da shugaban tashar DW Peter Limbourg, bayan wata tattaunawa ta keke da keke a gefen taron kafafan yada labaru na duniya, GMF 2015, a birnin Bonn.
Taron GMF 2012
A hagu Faruk Dalhatu shugaban Dandali Kura, Maiduguri Najeriya, Mohammad Nasiru Awal, DW Hausa (a tsakiya) da shugaban Sashen Hausa Thomas Mösch a zauren taron GMF na 2012 a Bonn.
Hawan jirgin ruwa a taron GMF
Bisa al'ada a kusan duk taron a kan ware rana guda a hau jirgin ruwa inda za a ci abinci, masu rawa su yi rawa daga yamma har cikin dare. A nan daga dama Abubakar Jijiwa tsohon babban daraktan tashar muryar Najeriya VON Abuja, Usman Shehu Usman DW Hausa da wakilinmu a Nijar Mahamane Kanta. Suna kan jirgin ruwa lokacin da yake yin bulaguro da baki
Taron GMF 2014: Liyafa a jirgin ruwa
Su ma mata mahalarta taron ba a barsu a baya ba a balaguro da jirgin ruwa, da a ciki ake shirya gagarumar liyafa ga bakin da suka halarci taron. A wannan hoto, a hagu: Halima Umar Saleh, Sa'a Ibrahim (tsakiya) sai Hauwa Abubakar Ajeje (dama), tsihuwar ma'aikaciyar Sashen Hausa na DW.
Jirgin ruwan balaguron GMF
Da wannan jirgin ruwa na kamfanin Köln/Düsseldorf Rheinenergie ake balaguron kammala taron GMF a kowace shekara.
Taron Global Media Forum 2020
Annobar Corona ta sauya yadda ake shirya taron GMF a 2020, inda ya gudana ta kafa sadarwa ta intanet. Taron ya duba tsarin zamani na "digital" a wajen yada labarai. Daga cikin wadanda suka ba da gudunmawa akwai Brang Mai, na Myitkyina News Journal, Myanmar da Nasir Salisu Zango, Freedom Radio, Kano, Najeriya da kuma David Schraven, na CORRECT!V, Germany.