Girka za ta rage kudin batarwar gwamnati | Labarai | DW | 16.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka za ta rage kudin batarwar gwamnati

Girka ta dauki wannan matakin ne a yayin da take fiskantar yarjejeniya mai tsauri da Kungiyar EU dangane da bashin da take so a taya ta biya.

Gwamnatin Girka ta bayyana cewa za ta sami wasu milliyoyin euro bayan ta rage yawan kudin batarwar gwamnati, da kuma kasafin kudin wasu ma'aikatu.

Duk da cewa yunkurin ba mai yawa ba ne, za ta sami akalla euro milliyan 300 a cewar mataimakin ministan kudi Dimitris Madras.

A daura da haka kuma, Madras ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa cewa za su kuma fara kai samame kan wadanda ke gudanar da irin aiyyukan da ke hana kasar samun irin kudin da ya kamata ta rika samu, wanda ya hada da sayar da mai a kasuwannin bayan fage a farashin da bai dace ba, da lalata tsarin kiwon lafiyar kasar da ma mafi mahimmanci wadanda ke kai kudade masu dimbin yawa a bankunan kasashen waje, a maimakon kasa ta yi riba daga jarin da za su zuba.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da take kokarin kammala yarjejeniyar da za ta samar ma ta da wani tallafin ceto kafin wa'adin da aka bata na gudanar da sauye-sauye, ranar 24 ga wannan watan na Afrilu