Girka za ta mika takardar neman karin lokaci | Labarai | DW | 18.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka za ta mika takardar neman karin lokaci

Girka ta tabbatar cewa a ranar Alhamis za ta aika takardar neman kara mata lokacin biyan bashi ga Eurogroup da ke tattauna batun wa'adin tallafin da aka ba wa kasar.

Gwamnatin Girka ta jaddada cewa a ranar Alhamis za ta mika takardar neman a tsawaita lokacin shirin tallafin da aka ba wa kasar. Kakakin gwamnati Gavriil Sakellarides ya ce za a aike takardar zuwa ga shugaban gungun Eurogroup Jeroen Dijsselbloem. Sai dai kakakin gwamnatin Girkar bai yi karin bayani kan abubuwan da takardar za ta kunsa ba. Hakan dai na nufin har yanzu ba a sani ba ko Girkar za ta amince da ka'aidojin da aka gindaya mata kawo yanzu. Ministan kudin Jamus Wolfgang Schäuble ya nuna bakin ciki ga abubuwan da ke faruwa baya-bayan nan inda ya ce:

"Dole ne Girka da ke samun wakilcin zababbiyar gwamnati ta demokradiyya ta yanke shawara kan abin da take so. Ba zan iya tsawaita abin da kasar ba ta bukata ba."

A ranar Jumma'a wa'adin da ministocin kudi na kasashe masu amfani da kudin Euro suka ba wa Girka na ta gabatar da sabuwar bukata zai kare. Sannan a ranar 28 ga watan nan na Fabrairu shirin ba ta bashi zai kare.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar